Lahadi 11 Oktoba 2026 - 14:08
Wani Labarin Soyayya Mai Cike da Bege: Tsiron Rayuwa a Gaza

Gaza/ A tsakanin tantunan yan gudun hijira a Gaza, inda yaƙi ya tarwatsa iyalai kuma ya mayar da gidaje baraguzai, Ibrahim da Maryam, duk da sun rasa dukkan danginsu, sun fara rayuwar aure da begen ganin kwanaki masu kyau nan gaba.

A cewar sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, labarin da ke ƙasa wani labarin soyayya ne daga cikin halin gudun hijira a Gaza; wurin da duk da rugujewa da rashin masoya, soyayya da bege har yanzu suna buɗe hanyar ci gaba da rayuwa.

A wani lungu na ɗaya daga cikin sansanonin yan gudun hijira a birnin Deir al-Balah, tsakiyar zirin Gaza, inda tantuna suke kama da juna ta fuskar launi, amma kowanne yana da nasa labarin rayuwa, farin ciki kaɗan yana ta bayyana a hankali.

A nan babu labarin ɗakin shagalin aure da aka ƙawata da furanni, babu kuma fitilun da ke jan hankali; amma muryar murna ta mata da ke fita daga tsakanin tantunan da suka tsufa, ta isa ta isar da sakon ga kowa: "A nan rayuwa tana ci gaba, kuma akwai soyayya da ba ta son dage farawarta."

A ranar da take ta musamman ga rayuwar Ibrahim, wannan saurayi dan shekara 26 ya auri Maryam, yar shekara 22, don fara rayuwar aure a karkashin rufin zane; wani farko da ya fara duk da dukkan wahalhalu da ɗacin gaskiyar al'amari.

Raunuka iri ɗaya da sabon bege

Labarin Ibrahim da Maryam ba labarin saduwa na matasa biyu kacal ba ne; labari ne na dunƙulewar raunuka biyu, waɗanda a inuwar tausayawa da soyayya, suke gab da warkewa.

Ibrahim shi ne kadai wanda ya tsira daga iyalinsa; iyalan da dukkansu suka rasu a wani harin sama da aka kai gidansu. Ya fito daga karkashin baragurbi, yayin da yake ɗauke da raunuka waɗanda alamunsu har yanzu suna jikinsa da ƙafarsa; ƙafar da yake jingina da ita lokacin da yake tafiya.

Haka ma Maryam ta fuskanci irin wannan bala'i. Gidan danginta ma an kai hari, kuma ita ce kaɗai ta tsira a cikin yan uwanta da mahaifanta. Maryam ta shafe watanni masu tsawo a asibiti don neman warkewar raunukan da suka samu jikinta.

Ibrahim, yayin da yake ƙara ƙaimi wajen kafa wani lungu na tantin da ya ƙafa tare da taimakon makwabtansa a sansanin, ya ce: "Lokacin da na rasa iyalina kuma ni ma na ji rauni, ina tsammanin rayuwa ta tsaya a wannan lokacin; amma lokacin da na ga yadda yanayin rayuwata da ta Maryam suke kama, sai na ji kamar Allah ya ba mu wata dama don mu sauya raunukanmu tare mu gina sabon iyali daga cikin toka."

Ya kara da cewa: "A wannan mawuyacin hali na tattalin arziki, ba mu iya gudanar da ɗaurin aure na al'ada ko siyan zinariya ba; amma mun amince da juna cewa don fara rayuwa, ba mu bukatar komai face gidan da zai haɗa mu da alƙawari na gaskiya a tsakaninmu."

A tantin da ke kusa, Maryam tana shirin ranar da take da muhimmanci a rayuwarta, tana dogara da ƙwarin gwiwarta. A lokaci guda, yan matan sansanin suna ta ƙoƙarin ƙera wani bouquet na fure daga takardu masu launi domin ba ta kyauta a matsayinta na amarya.

Maryam, yayin da take kallon tufafin al'ada da sauki da take shiryawa don wannan rana, ta ce: "Dukkanmu muna da raunukan da ba za su taba mantuwa ba a jikinmu da kuma a tunaninmu. Mun rasa iyali, gida, da komai; amma mun zabi kada mu zama bayi ga baƙin ciki da rashin abin da muka rasa."

Ta ci gaba da magana da murya mai ƙarfi: "Mun sani babu motocin da za su raka mu zuwa gidan aure; amma farin cikin da muke gani a idanun makwabtanmu a yau a sansanin, yayin da suke taimaka mana wajen shirya tantinmu, ya fi kowane irin ado gaskiya da ɗorewa."

Maryam ta ƙara da cewa: "Muna son mu tabbatar wa kanmu da duniya baki ɗaya cewa, ba zai yiwu a karya mu ba, kuma wannan tantin wucin gadi ne har sai Gaza ta koma ga kwanakinta na baya."

Labarin Ibrahim da Maryam ya nuna irin juriyar matasan da suka tsira a zirin Gaza; wani tsararraki da duk da mafi wahalar yanayi, suke dagewa wajen sake fasalta ma'anar kwanciyar hankali da zaman lafiya a rayuwa.

Ƙananan bayanai na wannan aure ba sakamakon yanayin rayuwa ba ne kawai; kamar nasara ce ta zahiri ta ruhin ɗan adam, inda ya sake tabbatar da cewa soyayya za ta iya shuka tsiron rayuwa kuma ta bude sabbin ƙofofin bege ga dan adam; ko a tsakanin baraguzai da tantuna.

Madogara: Kamfanin Dillancin Labaran Safa na Falasdinu

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha